19 Janairu 2026 - 08:44
Source: ABNA24
Gobarar Daji Tayi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 18 A Chile + Bidiyo

Mutane 18 ne suka mutu a wata gobarar dajin a kasar Chile

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Gobarar ta auku a yankunan dajin mafi girma wanda ya kasance a yankunan Noble da Biobio, ya zuwa yanzu ya tilasta wa mutane 20,000 tserewa daga gidajensu.

Gwamnatin Chile ta ayyana dokar ta baci a wadannan yankuna biyu. Rahotanni sun ce gobarar ta kone dajin da ya kai kimanin hekta 8,500 kuma ta lalata gidaje akalla 250.

Your Comment

You are replying to: .
captcha